Isa ga babban shafi
China-Koriya ta Arewa

Kim Jong Un ya gana da Xi na China

Shugabanin China da Koriya ta Arewa  Xi Jinping da  Kim Jong-un
Shugabanin China da Koriya ta Arewa Xi Jinping da Kim Jong-un CCTV / AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

China ta yiwa shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un kyakkyawar tarbo a ziyarar sa ta farko zuwa Beijing tun bayan hawa karagar mulkin kasar Koriya ta Arewa.

Talla

Shugaba Kim da mai masaukin sa Xi Jinping sun tatauna a tsakanin su, inda suka yaba kan kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Koriya ya ce babu tantama ziyarar sa ta farko zuwa kasar waje ba zata wuce kasar ta China ba, saboda muhimmancin ta a gare su.

Shugaba Xi ya ce zai cigaba da tuntubar shugaban na Koriya akai akai domin tabbatar da dorewar dangantakar dake tsakanin su.

Kamfanin dillancin labaran China ya ruwaito shugaba Kim na bayyana aniyar sa ta ganawa da shugabannin Amurka da Koriya ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.