Isra'ila

Netanyahu ya soke yarjejeniyar tsugunar da 'yan Afrika a Isra'ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Amir Cohen

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya sake duba matakin da ya dauka na soke yarjejeniyar tsugunar da dubban ‘yan gudun hijirar Afrika da ke samun mafaka a kasar. Netanyahu ya dauki matakin ne sakamakon caccakar da yake sha a gida jim kadan da  cimma yarjejeniyar a jiya Talata.

Talla

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta samu labarin cewa, Netanyahu ya soke yarjejeniyar da ya cimma da ita a ranar 2 ga watan Aprilu don samar da mafita ga ‘yan asalin kasashen Eritrea da Sudan da ke samun mafaka a Isra’ila.

Mai Magana da yawun Hukumar , William Spindler ya ce, za su ci gaba da amanna da wannan yarjejeniya da za ta amfani Isra’ila da kasashen duniya da kuma mutanen da ke bukatar mafaka, yayin da hukumar ke cewa tana fatan nan kusa Netanyahu zai janye matakinsa.

An dai cimma yarjejeniyar ce da zimmar dakile mayar da dubban ‘yan Afrika da karfi kasashensu na asali.

Sai dai Netanyahu ya yi amai ya lashe bayan da cewa da kansa ne ya sanar da kulla wannan yarjejeniya ta kafar Talabijin a yammacin jiya Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI