Isa ga babban shafi
facebook

An tatsi bayanan mutane miliyan 87 a Facebook

Shugaban Facebook, Mark Zukerberg ya bada hakuri kan tatsar bayanan jama'a da ke amfani da kafar
Shugaban Facebook, Mark Zukerberg ya bada hakuri kan tatsar bayanan jama'a da ke amfani da kafar REUTERS/Stephen Lam
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Kamfanin Facebook ya ce, akalla bayanan asirin masu amfani da shi miliyan 87 kamfanin Cambridge Analytica na Birtaniya ya tatsa.

Talla

Sabon adadin ya zarce miliyan 50 da aka bayar a baya, wanda ya jefa masu amfani da dandalin na Facebook cikin damuwa dangane da bayanansu.

Wadannan bayanai na zuwa ne lokacin da kamfanin ke gabatar da sabbin matakan kare bayanan jama’ar da ke mu’amala da shi.

Mike Schroepfer, babban jami’in kula da fasahar kamfanin ne ya bada wannan sabon adadi, wanda ya ce, ya shafi akasarin mutanen da ke Amurka.

Ana ganin tatsar bayanan nada nasaba da yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.