Korea ta kudu

Kotu ta daure tsohuwar Shugabar kasar Koriya ta kudu

Wata Kotu a kasar Koriya ta Kudu ta samu tsohuwar shugabar kasar Park Guen Hye da laifin cin hanci da rashawa da kuma amfani da ofishin ta ta hanyar da bata kamata ba.

Park Guen Hye tsohuwar Shugabar kasar Koriya ta kudu
Park Guen Hye tsohuwar Shugabar kasar Koriya ta kudu REUTERS/Kim Hong-Ji
Talla

Alkalin kotun, Kim Se-yoon ya ce Hye tayi amfani da mukamin ta wajen tilastawa kamfanoni bada tallafin Dala miliyan 72 ga wasu gidauniyoyi biyu dake karkashin wata kawar ta Choi Soon-Sil.

Kotun ta bayyana hukuncin daurin shekaru 24 a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI