Myanmar

An daure sojin Myanmar saboda kashe Musulmai

Wasu daga cikin sojin Myanmar a jihar Rakhine mai fama da tashin hankali
Wasu daga cikin sojin Myanmar a jihar Rakhine mai fama da tashin hankali STR / AFP

Mahukuntan Myanmar sun daure sojoji bakwai a gidan yari sakamakon samun su da hannu a kisan wasu Musulman Rohingya 10 a ranar 2 ga watan Satumban bara a kauyen Inn Din.

Talla

Babban hafason tsaron kasar, Janar Min Aung Hlaing ya ce, tuni aka tube wa sojojin kaki tare da yi mu su daurin shekaru 10 a gidan kaso, in da kuma za su rika yin ayyukan wahala a taswon wa’adin shekarun.

A karon farkon kenan da jami’an sojin Myanmar suka amsa laifi a zargin da ake yi mu su na murkushe al’ummar Musulmi da ke rayuwa a jihar Rakhine, lamarin da ya tilasta wa kimanin mutane dubu 700 neman mafaka a Bangladesh.

Sai dai duk da samun jami’an da aikata laifi, har yanzu rundunar sojin kasar na ci gaba da bayyana ‘yan Rohingya a matsayin ‘yan ta’adda, amma babu wata sheda da ta gabatar da ke tabbatar da ikirarinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.