Isa ga babban shafi
facebook

Rashawa na kai wa Facebook hari

Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg
Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Shugaban shafin Facebook, Mark Zuckerberg ya shaida wa mambobin Majalisar Dattawan Amurka cewa, kamfaninsa na fafatawa da wasu mutanen Rasha da ke kokarin amfani da dandalin na facebook don cimma muradinsu.

Talla

Zuckerberg ya ce,wannan yaki ne da makami, kuma Rashawan za su ci gaba da inganta ayyukansu.

Zuckerberg da ke shan tambayoyi kan kutsen bayanan sirrin mutane miliyan 50 a shafin facebook, ya kuma ce, Robert Mueller da ke binciken zargin kutsen Rasha a zaben Amurka, ya yi wa ma'aikatan kamfanin wasu tambayoyi.

Ko da yake shugaban na Fcebook ya ce, ba ya cikin wadanda aka yi wa tambayoyin.

A bangare guda, Zuckerberg ya nemi afuwa dangane da yadda aka saci bayyanan milyoyin mutanen da ke amfani da shafin ba tare da saninsu ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.