Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta gargadi Amurka kan Syria

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Maxim Shipenkov/Pool via REUTERS
Zubin rubutu: Faruk Yabo | Ahmed Abba
2 Minti

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce, duk wani harin da kasashen yammacin Duniyar za su iya kaiwa a Syria na iya tada mummunan tashin hankali a tsakaninsu.

Talla

Putin ya fadi hakan ne a yayin da yake zantawa da takwaransa na Iran Hassan Rouhani ta wayar Tarho, kwana daya bayan da Amurka ta jagoranci kai hari a kasar Syria.

Shugabannin guda biyu dai na ganin harin da Amurka ta jagoranta na iya hana batun shawo kan matsalar cikin ruwan sanyi.

A ranar Asabar da ta gabata ne Kasar Amurka da Faransa da kuma Burtaniya suka kai hari ga gwamnatin Bashar al-Assad, mako guda bayan da aka zarge shi da amfani da makami mai guba kan fararen hula a yankin Douma da ke gabashin birnin Damascus.

Kasar Syria dai ta dade tana musanta zargin da kasashen Duniya ke yi mata na amfani da makami mai guba ga fararen Hula, harma abokiyar kawancenta Rasha na cewar 'yan tawayen da kansu ne ke amfani da makami mai guba.

Rasha dai ta bayyana a fili cewar kara kai wa Syria harin da Amurka ke jagoranta, na a matsayin harzuka tashin fada ne tsakaninsu da Syria kasa mai cikakken iko.

Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya dai ya aika Ayari mai karfi daga kungiyar nan mai fafutukar hana amfani da makami mai guba ga kasashen Duniya, domin gudanar da bincike akan gaskiyar al'amari.

Kasashe da dama ne suka nuna rashin jin dadinsu akan yadda Amurka da kawayenta suka kai wa Syria harin ba-zata, ciki kuwa harda kasar Aljeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.