Rasha-Syria

Rasha ta musanta lalata hujjar amfani da makami mai guba a Syria

A cewar Amurka Rasha ta isa yankin da ake da hujjar kai hari da makamin mai guba tare da lalata duk wata hujja da za ta tabbatar da gaskiyar harin.
A cewar Amurka Rasha ta isa yankin da ake da hujjar kai hari da makamin mai guba tare da lalata duk wata hujja da za ta tabbatar da gaskiyar harin. REUTERS/Bassam Khabieh

Gwamnatin Rasha ta yi watsi da zargin cewar ta lalata shaidun da ke nuna cewar shugaba Bashar al Assad na Syria ya yi amfani da makami mai guba a Douma da ke kasar Syria.

Talla

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi watsi da zargin da kasar Amurka ta yi wa kasarsa cewar Rasha ta lalata shaidar da ke tabbatar da amfani da makamin mai guba domin hana masu bincike tabbatar da zargin da ake wa kasar.

Yayin gudanar da wani taro na kungiyar da ke yaki da yaduwar makamai masu guba a birnin Hague, Jakadan Amurka Ken Ward ya shaidawa mahalarta taron cewar, jami’an Rasha sun isa inda aka kai harin da makami mai guba, kuma sun lalata shaidar da ke wurin kafin ziyarar kwararun masu bincike.

Jakadan ya ce muddin wannan zargi ya tabbata, matakin zai yi matukar illa ga binciken da ake shirin gudanarwa.

Shugaban hukumar yaki da yaduwar makamin mai guba, Ahmet Uzumcu, ya ce har yanzu jami’an sa da suka isa Syria domin gudanar da bincike basu samu damar zuwa Douma ba, domin gudanar da aikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.