Bakonmu a Yau

Bakonmu A Yau Dr Sani Yahaya Janjuna

Sauti
Motar kwararru masu binciken makami mai guba daga Majalisar dinkin Duniya
Motar kwararru masu binciken makami mai guba daga Majalisar dinkin Duniya REUTERS/Omar Sanadiki

Yanzu haka dai kasashen Yammacin Duniya na cigaba da zargin Rasha da lalata shaidun da ke tabbatar da cewa an yi amfani da makami mai guba kan fararen hula a garin Douma da ke kasar Syria, zargin da Rashan ta musanta.

Talla

Wasu kwararru kan sha’anin tsaro na ganin cewa abu ne mai wuya a ce Bashar Assad ya yi amfani da makami mai guba, a daidai lokacin da dakarunsa suka yi nasarar kwace illahirin yankunan kasar daga hannun ‘yan tawaye da kuma sauran ‘yan bindiga.

A game da wannan lamari ne Mahamman Salisu Hamisu, ya zanta da Dr Sani Yahaya Janjuna, mai sharhi kan lamurran yau da kullum daga birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ga kuma zantawarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.