Syria

Masu binciken makami mai guba sun isa a birnin Douma na Syria

Wata kafar watsa labarai ta cikin gida a kasar Syria ta ruwaito cewar kwararru masu binciken makami mai guba daga kwamitin kwararru na Majalisar dinkin Duniya sun isa a birnin Douma na kasar Syria a yau dinnan.

Masu binciki kan makamai masu guba na (OPCW) sun sauka a Douma kasar Syria.
Masu binciki kan makamai masu guba na (OPCW) sun sauka a Douma kasar Syria. 路透社。
Talla

Birnin Douma dai birni ne da ke a wajen birnin Damascus inda aka zargi Sojin Gwamnati da amfani da makamai masu guba a kwanakin goma da suka gabata, harin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane da dama.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Syria mai suna SANA ya bayyana cewar mambobin kwamitin ma’ana na kungiyar nan mai fafutukar hana amfani da makamai masu guba ta Majalisar dinkin Duniya, sun sauka a birnin Douma yau dinnan.

Samun rahotannin amfani da makamai masu gubar da aka yi a birnin Douma na Syria a ranar 7 ga watan Afrilu ne ya janyo farmakin hadin guiwa da Amurka da Faransa da Burtaniya suka kai wa Syria a karkashin jagorancin kasar Amurka.

Kasashen dai sun zargi shugaba Bashar al-Assad na Syria ne da amfani da karfin Soji da ya wuce kima, musamman na kai hari da makami mai guba.

A wannan lokacinda aka zargi gwamnatin kasar Syria da amfani da guba a Douma dai an hakikance cewar birnin na a hannun ‘yan tawaye ne, amma wannan harin ne ya haddasa shigar birnin a hannun dakarun Gwamnati.

Harin da aka yi amannar an kai shi ne ba tare da tabbacin cewar dakarun Gwamnatin ne suka kai harin, ya auku ne a yayin da ake dakon ganin jami’an da Majalisar dinkin Duniya ta kafa sun isa a Syria tare da gudanar da aikinsu kamin a tabbatar da zargin da ake yi wa Gwamnatin.

A ranar Talata dai harin da Amurka ta jagoranta zuwa kasar Syria ya gamu da kalubalen al’ummar Duniya musamman lura da yadda Amurka ta yi riga-malam Masallaci na kai hari a Syria babu tabbas akan zargin da suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI