Amurka

Barbara Bush,mahaifiyar tsohon Shugaba Bush ta rasu

Barbara Bush mahaifiyar tsohon Shugaban Amurka Georges W Bush
Barbara Bush mahaifiyar tsohon Shugaban Amurka Georges W Bush REUTERS/Jason Reed

Matar tsohon shugaban Amurka Barbara Bush wadda ta haifi shugaba George Bush ta rasu tana da shekaru 92 a duniya, bayan tayi fama da rashin lafiya.Tuni al’ummar kasar suka fara aikewa da sakonnin ta’aziyar su ga iyalan tsoffin shugaban kasar.

Talla

Shugaban ma’aikatan tsohon shugaban kasa George Bush, Jean Becker ya bayyana cewar, mai gidan nasa mai shekaru 93 ya kwashe dogon lokaci kusa da Barbara Bush kafin rasuwar ta, kuma yanzu haka yana cikin yanayin zaman makoki.

Becker yace nan gaba kadan za’a bayyana shirin jana’izar Barbara Bush wadda ta bar yara 5, cikin su harda tsohon shugaban kasa George Bush da jikoki 17 da kuma yayan su guda 7.

Bayani sun ce tsohon shugaban kasar ya gamu da Barbara ce lokacin tana da shekaru 16, shi kuma yana da shekaru 17, lokacin suna karatu a Massachusetts, kuma sun yi aure a shekarar 1945, lokacin da yake hutu daga aikin soji.

Cikin wadanda suka aike da sakonnin ta’aziyar su sun hada da shugaba Donald Trump da tsohon shugaban kasa Barack Obama da tsohuwar Sakatariyar harkokin waje Madeleine Albright da Sanata John McCain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.