Isa ga babban shafi
Cuba

Miguel Diaz-Canel ya zama shugaban kasar Cuba

Shugaba Raul Castro a hagu mataimakinsa haka kuma sabon shugaban kasar cuba Miguel Diaz-Canel daga dama
Shugaba Raul Castro a hagu mataimakinsa haka kuma sabon shugaban kasar cuba Miguel Diaz-Canel daga dama AFP
Zubin rubutu: Salissou Hamissou
1 Minti

Nadin da aka yi wa mutum na biyu mafi girman mukami a kasar dan shekaru 57 a duniya, a jiya laraba ne aka gabatar wa yan majalisar dokokin da suka kada kuri’ar amincewa da shi.

Talla

A lokacin da aka sanar da takararsa shi kadai a mukamin shugabancin kasar ta Cuba, Miguel Diaz-Canel da wanda ya gada, Raul Castro mai shekaru 86 a duniya sun rungume juna cikin farin ciki abinda jama’ar kasar suka share tsawon watanni suna jiran ganin faruwarsa

Tun a bara ne dai ake ta rade radin cewa Miguel Diaz-Canel ne zai dana kujeran mulkin kasar, bayan da shi shugaban mai barin gado ya sanar da cewa shi da kansa ne ya zabi mataimakinsa domin maye gurbinsa kan mukamin shugabancin kasar ta Cuba.

Sabon shugaban dai ya kasance shugaban kasar na farko da bashi da halaka da gidan su Castro.

Tun shekara ta 1959 lokacin da tsohon shugaba Fidel Castro ya kwace mulkin kasar ta hanyar sunkuru, alummar Cuba ba su san abinda ake cewa mika mulki ba, sai a lokacin da rashin lafiya ta tilasta wa fidel Castro din sauka daga kan kujerar mulkin ta hanyar nada kanensa kan matsayin cewa da Raul a shekara ta 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.