Syria

Lafarge ya bai wa mayakan Syria makuden kudade

Ana zargin kamfanin Lafarge na Faransa da bai wa 'yan bindiga Dala miliyan 6 don gudanar da ayyukansa a Syria ba tare da tsangwama ba
Ana zargin kamfanin Lafarge na Faransa da bai wa 'yan bindiga Dala miliyan 6 don gudanar da ayyukansa a Syria ba tare da tsangwama ba Reuters/Gonzalo Fuentes

A ci gaba da bankado bayanai dangane da zargin da ake yi wa reshen kamfanin simitin Lafarge na Faransa a kasar Syria, an ruwaito cewa kamfanin ya biya makudden kudade ga mayakan jihadi domin samun damar gudanar da ayyukansa a kasar mai fama da rikici.

Talla

Jaridun Faransa Liberation da kuma Le Monde sun ruwaito cewa tsakanin 2012 zuwa 2014, Lafarge ya zuba wa masu dauke da makamai a Syria sama da Dala milyan 6 a sassan kasar.

Rahoton ya ce, akalla Dala dubu 500 na wadannan kudade an mika su ne ga kungiyoyin da ke ikirarin jihadi.

Le Monde da kuma Liberation sun ce, sun samu wadannan bayanai ne kunshe a wasu muhimman takardu da ke karin bayani kan yadda aka zuba kudaden lokacin da Kotu ke bincike a kai, lamarin da ya sa duk da janyewar kamfanonin kasashen duniya daga yankunan da ke hannun ‘yan bindiga amma kamfanin ya ci gaba da ayyukansa ba tare da wata tsangwama ba.

Jaridun sun bayyana cewa Hukumar Tara Bayanan Sirrin Faransa na da masaniya kan haka, kuma wani mai suna Jean-Claude Velard wanda tsohon sojin ruwa ne ya sha sanar da mahukuntan Faransa wannan alaka da ke tsakanin kamfanin da ‘yan bindiga, to amma ba su ce komai ba a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.