Syria

Sabon rikicin ya kaure a Deir Ezzor na kasar Syria

A kasar Syria an samu wani karo tsakanin dakarun gwamnatin kasar da mayakan da Amurka ke marawa baya, wanda yayi sanadiyar kashe mutane 15.Kungiyar dake sa ido kan rikicin Syria, mai cibiya a London, tace an samu rikicin ne a Deir Ezzor inda aka kashae mutane 9 daga bangaren sojojin gwamnati, yayin da 6 suka mutu daga bangaren mayakan.

Yakin kasar Syria ya tilastawa mutane tserewa daga gidajen su
Yakin kasar Syria ya tilastawa mutane tserewa daga gidajen su REUTERS/Omar Sanadiki
Talla

Kamfanin dillancin labaran Sana ta ruwaito cewar sojojin gwamnatin Syria sun yi nasarar kwace kauyuka 4 a gabashin kasar daga hannun mayakan Kurdawa.

Wannan sabon fada na zuwa ne a dai dai lokacin da Shugaban kasar Bashar Al Assad ke ci gaba da samun goyan bayan yan kasar, a makon da ya gabata dubban 'yan kasar sun gudanar da zanga-zangar nuna goyan bayan ga shugaba Bashar al-Assad a birnin Damascus, bayan harin da wasu kasashen yammacin duniya suka kai wa kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI