Isa ga babban shafi
Syria

Birtaniya ta hallaka fararen hula a Syria

Wasu fararen hula kenan lokacin da suke tserewa hare-haren bama-bamai ta sama a Syria.
Wasu fararen hula kenan lokacin da suke tserewa hare-haren bama-bamai ta sama a Syria. Abdulmonam Eassa/AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Birtaniya ta tabbatar da yadda wasu hare-harenta ta sama suka hallaka dimbin fararen hula a Syria. Sanarwar da ta fitar ta ce harin ya nufaci maboyar mayakan IS ne amma kuma aka kuskure tare da yin luguden wuta kan fararen hula.

Talla

Wananna ne dai karon farko da Birtaniyar ta amsa laifinta na kai hari tare da hallaka fararen hular da basu ji ba basu gani ba, ko da ya ke dai a lokuta da dama tana dora laifin hakan kan gwamnatin Syria.

Sanarwar wadda Sakataren tsaron birtaniyar Gavin Williamson ya fitar, ta nuna cewa ko a ranar 26 ga watan Maris ma wasu jerin hare-haren birtaniyar a Maboyar mayakan IS 3 da ke yankin gabashin Ghouta sun hallaka wani mai babur da ya zo giftawa ta wajen.

Sanarwar Birtaniyar na zuwa ne bayan wata kafar yada labarai ta kwarmata yadda hare-haren na ta ke salwantar da rayukan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.