Isa ga babban shafi
WHO

Fiye da kaso 90 na al'ummar duniya na shakar gurabatacciyar Iska- WHO

Rahotan ya ce shaker irin wannan iskar kan haifar da shanyewar jiki ko sankara ko kuma cutar nimoniya.
Rahotan ya ce shaker irin wannan iskar kan haifar da shanyewar jiki ko sankara ko kuma cutar nimoniya. LA Bagnetto
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da kashi 90 na jama’ar duniya na shaker iskar da aka gurbata, wanda hakan ke yin sanadiyar mutuwar mutane miliyan 7 kowacce shekara.

Talla

Sabon rahotan Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce kowanne sako na duniya na fama da matsalar gurbatar muhalli, amma kuma matsalar tafi kamari a Yankunan da kae fama da talauci.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus yace gurbata muhallin na barazana ga daukacin mutanen duniya, amma kuma talakawa sun fi shan kudar matsalar.

Binciken da hukumar ta gudanar wanda ya duba matsalar gurbata muhalli a waje da cikin gidaje, yace akalla mutane miliyan 7 ke mutuwa kowacce shekara saboda shakar iskar da aka gurbata.

Rahotan ya ce kashi 90 na masu mutuwa sakamakon cutar dake da nasaba da numfashi na zuwa ne daga kasashe matalauta dake Asia da Afirka.

Rahotan ya ce shaker irin wannan iskar kan haifar da shanyewar jiki ko sankara ko kuma cutar nimoniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.