Isa ga babban shafi
Syria

Za a zurfafa bincike kan amfani da guba a Dhouma

Wani yankin Syria dake fama dake hannun yan tawaye
Wani yankin Syria dake fama dake hannun yan tawaye REUTERS/Omar Sanadiki
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Jami’an hukumar Majalisar dinkin Duniya da ke hana amfani da makamai masu guba za su tono kaburburan mutanen da ake zargin cewa sun mutu ne sakamakon shakar iskan gas mai guba a yankin Douma da ke Syria.

Talla

Shugaban hukumar Ahmed Uzumcu, ya ce bayan tono gawarwakin mamanta da yawansu ya kai 40, kwararri za su gudanar da gwaje-gwaje domin kawar da shakku kan wannan lamari da ya faru a ranar 7 ga watan afrilun da ya gabata.

Birnin Douma dai birni ne da ke a wajen birnin Damascus inda aka zargi Sojin Gwamnati da amfani da makamai masu guba a kwanakin da suka gabata, harin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane da dama.

Samun rahotannin amfani da makamai masu gubar da aka yi a birnin Douma na Syria a ranar 7 ga watan Afrilu ne ya janyo farmakin hadin guiwa da Amurka da Faransa da Burtaniya suka kai wa Syria a karkashin jagorancin kasar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.