Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Tarayyar Turai za ta hana takunkuman Amurka tasiri a Iran

Faransa ce dai za ta zama ja gaba wajen ganin kasashen na Turai sun ci gaba da mutunta yarjejeniyar Nukiliyar ta Iran.
Faransa ce dai za ta zama ja gaba wajen ganin kasashen na Turai sun ci gaba da mutunta yarjejeniyar Nukiliyar ta Iran. 路透社。
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu | Nura Ado Suleiman
Minti 2

Faransa, ta ce kasashen Turai za su dauki matakan kare kamfanoninsu, daga takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka za ta mai da kan kasar Iran da kawayenta. Faransa ta mayar da martanin ne sa’o’i kadan, bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Talla

Duk da cewa matakin da shugaba Donald Trump ya dauka bai zo a bazata ba, baki dayan ministocin kasashen tarayyar Turai sun yi kakkausar suka ga janyewar ta Amurka, abinda suka bayyana a matsayin barazana ga tsaron duniya.

Shugabar ofishin kare manufofin kungiyar Tarayyar Turai a kasashen ketere Federica Mogherini kira ta yi ga sauran kasashen duniya da su cigaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar ta Iran.

Mogherini ta ce yarjejeniyar ta shafi dukkanin kasashen duniya, kuma ta na aiki yadda ya kamata a don haka kwalliya ta na biyan kudin sabulu dangane da manufar da yasa aka kafa ta.

Don haka a cewarta Tarayyar Turai za ta dauki dukkanin matakan da suka dace don cigaba da kare wanzuwar yarjejeniyar inda ta ce akwai bukatar kasashen da ke cikinta su cigaba da mutuntata.

Sai dai a nasa bangaren Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yabawa Donald Trump ya yi a bisa janyewar Amurka daga yarjejeniyar ta Nukiliyar Iran, inda ya ke cewa Isra’ila na mika tarin godiya ga shugaban bisa jarumtakarsa.

A mako mai kamawa ne Ministocin harkokin waje na kasashen Tarayyar Turai za su gana da takwaransu na kasar Iran Muhd Javad Zariff domin jaddada masa matsayar kasashensu na daukar matakan cigaba da kare yarjejeniyar da kuma hana takunkuman karya tattalin arzikin Amurka tasiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.