Isa ga babban shafi
Iran

Ba ma fatan barkewar sabon rikici a gabas ta tsakiya - Rouhani

Kalaman na Rouhani na zuwa ne bayan harin da Isra'ila ta kai kan dakarun Iran da ke yaki da ta'addanci a Syria.
Kalaman na Rouhani na zuwa ne bayan harin da Isra'ila ta kai kan dakarun Iran da ke yaki da ta'addanci a Syria. REUTERS/Danish Siddiqui
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Shugaban Iran Hassan Rohani ya ce kasarshi ba ta fatan barkewar wani sabon tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. Rohani na zantawa ne ta wayar tarho da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kwana daya bayan farmakin da Isra’ila ta kai wa dakarun Iran a cikin Syria.

Talla

Shi ma dai Babban magatakarda na MDD Antonio Guterres ya bukaci bangarorin biyu da su guji tsokanar juna da za ta iya jefa yankin Gabas ta Tsakiya a cikin yanayi na fito na fito.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, ya ce lura da halin da ake ciki a Syria, da janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya, da kuma fito-na-fito tsakanin Iran da Isra’ila, za a iya cewa lamurra na dada rincabewa ne a yankin na Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.