Isa ga babban shafi
Indonesia

'Yan kunar bakin wake sun sake kai hari a Indonesia

Jami'an 'yan sandan Indonesia na cikin shirin ko ta kwana bayan hare-haren da aka kai wa kasar a cikin kwanaki biyu
Jami'an 'yan sandan Indonesia na cikin shirin ko ta kwana bayan hare-haren da aka kai wa kasar a cikin kwanaki biyu Antara Foto/ Didik Suhartono / via REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Azima Bashir Aminu
Minti 2

Wasu 'yan kunar bakin wake 4 akan babura sun tada bam a shalkwatan 'yan Sandan birnin Surabaya da ke kasar Indonesia, in da suka raunana jami’ai akalla 10, bayan sun hallaka kansu.

Talla

Harin na yau na zuwa ne kwana guda da wasu bama-bamai suka tashi a wasu mujami’u da ke birnin na Surabaya  wanda IS ta dauki alhaki, abin da ya sa shugaba Joko Widodo ya sake jaddada matsayinsa na ci gaba da yaki da ta’addanci.

Rahotanni na cewa mutane shiddan da suka kaddamar da hare-hare a majami’un kasar uku lokacin da ake tsaka da ibada sun fito ne daga gida guda, lamarin da ya yi sanadiyar salwantar rayuka 13 da kuma  jikkatar gwammai.

Mutanen 6 sun hada da maza da mata kuma mambobi ne a kungiyar ISIS.

Wasu rahotanni da kafofin yada labaran kasar suka fitar na nuni da cewa iyalan sun dawo ne daga kasar Syria bayan fatattakar da suka fuskanta daga dakarun hadaka.

An dai bayyana mutanen shida da uwa da uba wadanda suka kai harin farko sai kuma maza biyu da shekarunsu bai wuce 16 da 18 ba, kana kuma kannensu mata masu shekaru 12 da 9.

Rahotanni sun ce matan biyu na sanye ne da hijabi da kuma mayanin fuska yayin da aka yi musu damara da bam a jikinsu, in da su kuma mazan biyu suka danna kai majami’ar haye a babur, sai kuma iyayen wadanda suka dasa bam din a harabar cocin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.