Isa ga babban shafi
Havana

Mutane 3 sun tsira a hadarin jirgin saman Cuba mai fasinja 110

Jirgin wanda ke dauke da fasinjoji akalla 104 ya fadi ne mintuna kalilan da tashinsa daga babbar tashar jirgin sama ta Havana.
Jirgin wanda ke dauke da fasinjoji akalla 104 ya fadi ne mintuna kalilan da tashinsa daga babbar tashar jirgin sama ta Havana. Adalberto ROQUE / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Wani jirgin Fasinja dauke da mutane 113 ya fadi a yammacin yau Juma’a jim kadan bayan da ya tashi daga babban filin jirgin saman Havana. Kawo yanzu dai rahotanni sun ce mutane uku aka iya tseratarwa da ransu daga cikin fasinjan 110. 

Talla

Jirgin kirar Boeing 737 ya fadi ne a tsakanin kauyukan Boyeros da kuma Santiago de La Vegas, mai tazarar kilomita 20 da babban filin jirgin saman na Havana.

Kawo yanzu dai ba a kai ga gano dalilin faduwar jirgin ba, amma mutanen da ke makwabtaka da wurin da jirgin ya fadi sun ce sun jiyo wani kara ne kafin daga bisani kuma bakin hayaki ya lullube sararin samaniya.

Rahotanni sun ce mutanen uku da aka iya cetowa da ransu na cikin mawuyacin hali yayinda ake basu kulawar gaggawa.

Shugaban kasar Miguel Diaz-Canel wanda ya ziyarci wajen faruwar lamarin ya ce tabbas mutane da dama sun rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.