G20

Taron G20 na tattaunawa kan kisan Falasdinawa

Taron G20 na wannan karo zai tattauna kan batutuwan da ke ci wa duniya tuwo a kwarya
Taron G20 na wannan karo zai tattauna kan batutuwan da ke ci wa duniya tuwo a kwarya Presidencia Argentina

Yaki da ta’addanci, matsalar sauyin yanayi, kashe Falasdinawa da sojojin Isra'ila suka yi da kuma batun yarjejeniyar nukiliyar Iran na daga cikin batutuwan da za su mamaye taron Ministocin Kungiyar Kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da aka fara yau a kasar Argentina.

Talla

Taron wanda aka saba gudanar da shi a tsakanin kasashen da ke cikin kungiyar, wannan karo zai gudana ne a Buenos Aires dake Argentina, in da zai mayar da hankalin kan manyan batutuwan da suka damu kasashen duniya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta ce taron zai dada karfafa dangantaka tsakanin kasashen da ke cikin kungiyar musamman kan batun yaki da ta’addanci da kuma sauyin yanayi.

Ga alama za a samu rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen da ke cikin kungiyar kan zaben Venezuela da Nicolas Maduro ya lashe da yarjejeniyar nukiliyar Iran da Amurka ta fice daga ciki da kuma kisan da sojojin Israila suka yi wa Falasdinawa sama da 100 a cikin mako guda.

Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Sullivan ke wakiltar Amurka a taron, wanda ake saran zai shata jadawalin batutuwan da shugabannin kasashensu za su tattauna a taron da za su yi a watan Nuwamba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.