Isa ga babban shafi
Rasha

ISIS ta kashe dakarun Rasha a Syria

Sojojin Syria da na Rasha na cikin shirin ko ta kwana bayan farmakin ya hallaka jami'ai 33
Sojojin Syria da na Rasha na cikin shirin ko ta kwana bayan farmakin ya hallaka jami'ai 33 Delil souleiman / AFP
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Wani kazamin hari da kungiyar ISIS ta kai a yankin gabashin Syria, ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Rasha da kuma dakarun gwamnatin Bashar al Assad da dama.

Talla

Bayan faduwar daular da ta yi ikirari a kasar Syria a bara, a yanzu kungiyar ISIS na rike da wata karamar tunga a wani yankin sahara da ya sadar da hanyar kan iyakar gabashin kasar.

A cikin makon jiya ne, mayakan ISIS din suka kaddamar da jerin hare-haren ba za ta akan dakarun gwamnatin kasar, in da suka kashe sojojin Rasha da kuma na Syria da dama a garin Mayadden da ke gabashin lardin Dier Ezzor.

Shugaban kungiyar da ke sa ido kan Syria mai cibiya a Birtaniya, Rami Abdel Rahman, ya shaida wa kamfanin Dillancin Labaran Faransa, AFP cewa, sojojin da ke goyon bayan gwamnatin Syria 33 ne ISIS ta kashe da suka hada da na Rasha.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce, jami’anta hudu aka kashe a farmakin na Dier Ezzor, kuma biyu daga cikinsu sun mutu ne nan take, yayin da sauran suka bar duniya bayan wata ‘yar jinya a asibitin sojin Syria, sannan kuma a halin yanzu akwai wasu uku da ke ci gaba da karbar magani.

Kasar Rasha da ta kasance aminiya ga Syria, ta taimaka wa gwamnatin Bashar al-Assad wajen karbe yankuna da dama daga hannun ISIS tun daga shekarar 2015 ta hanyar kaddamar da hare-haren sama da na kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.