Isa ga babban shafi
Colombia

Jam'iyyar adawa ta yi nasara a zaben Colombia

Ivan Duque na jam'iyyar adawa ya samu kusan kashi 40 na kuri'un da aka kada a zaben Colombia, in da ya kere wa dan takarar jam'iyya mai mulki
Ivan Duque na jam'iyyar adawa ya samu kusan kashi 40 na kuri'un da aka kada a zaben Colombia, in da ya kere wa dan takarar jam'iyya mai mulki REUTERS/Carlos Garcia Rawlins

Jam'iyyar da ke adawa da kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar 'yan tawayen FARC a kasar Colombia ta lashe zaben shugaban kasar zagaye na farko da aka yi, sai dai ba ta samu kashi 50 din da ake bukata domin ba ta damar kafa gwamnati ba, abin da zai tilasta ta zuwa zagaye na biyu.

Talla

Dan takarar jam’iyyar da ke adawa da gwamnati mai ci, Ivan Duque ya lashe kusan kashi 40 na kuri’un da aka kada, yayin da Gustavo Pedro da ke yi wa jam’iyya mai mulki takara ya samu kashi 25 a kuri’ar da ta raba kan al’ummar kasar kan makomar yarjejeniyar zaman lafiyar da shugaba Juan Manuel Santos ya kulla.

Wannan dai shi ne zabe na farko a cikin shekaru 50 da aka gudanar da shi ba tare da barazanar tashin hankali daga tsohuwar kungiyar 'yan tawayen FARC da ta rikide ta zama jam’iyyar siyasa ba.

Shugaban hukumar zaben kasar, Juan Carlos Galindo ya ce, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, yayin da ya bada adadin wadanda suka kada kuri’a zuwa sama da kasha 53.

Shugaba Juan Manuel Santos mai barin gado ya yaba da yadda zaben ya gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.