Turai- Venezuela

EU ta amince da sanya takunkumi kan Venezuela

Kasashen duniya sun yi tir da nasarar da Nicolas Maduro zai ya samu a zaben Venezuela saboda zargin rashin sahihancinsa
Kasashen duniya sun yi tir da nasarar da Nicolas Maduro zai ya samu a zaben Venezuela saboda zargin rashin sahihancinsa REUTERS/Marco Bello

Ministocin Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da shirin saka takunkumi kan duk jami’an da ke da hannu a zaben da ya sake bai wa shugaba Nicolas Maduro nasara  a Venezuela, zaben da Ministocin suka bayyana a matsayin mara inganci.

Talla

A taron da suka saba yi a birnin Brussels, Ministocin Kasashen Turai 28  sun amince da fara aiki akan abin da suka sanya a gaba na saka takunkumi ga daukacin jami'an hukumar zaben kasar a cikin watan Yuni.

Daukar wannan matakin na zuwa ne bayan da kungiyar ta fada a makon da ya shude cewar, suna shirin daukar mataki akan shugaba Nicolas Maduro saboda zaben da aka yi ba mai inganci ba ne.

Kungiyar dai ta kuduri aniyar daukar mataki cikin hanzari bisa tanadin la’akari da ka’idojin kungiyar, amma ba tare da sun bari al’ummar kasar sun shiga matsala ba.

Shugaba Maduro ya yi nasara da akalla kashi 68 na kuri’un zaben da aka gudanar a cikin watan Mayu, zaben da ‘yan adawar kasar suka kaurace wa.

Daga cikin wadanda kungiyar ke kokarin saka wa takunkumin har da manyan jami’an gwamnatin kasar 7 da suka hada da tsohon Ministan Harkokin cikin gida na kasar ta Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.