Isa ga babban shafi
amurka-Turai

Amurka za ta fara karbar harajin karafa daga Turai

Gwamnatin Donald Trump ce ta bullo da sabon tsarin karbar harajin karafa da samfolo da ake shigowa da su daga kasashen Turai da Canada da Mexico
Gwamnatin Donald Trump ce ta bullo da sabon tsarin karbar harajin karafa da samfolo da ake shigowa da su daga kasashen Turai da Canada da Mexico REUTERS/Kevin Lamarque/
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Amurka ta ce daga gobe juma’a za ta fara aiki da sabon tsarin biyan harajin karafa na 25% da kuma 10% na samfolo akan kasashen Turai da Canada da kuma Mexico.

Talla

Sakataren Ma’aikatar Kasuwanci ta Amurka Willbur Ross, shi ne ya sanar da hakan a yau, abin da ke tabbatar da cewa Amurka ba ta da niyar ja da baya a game da wannan batu da ka iya jefa ta rikicin kasuwanci da kasashen na Turai.

Mr. Ross ya ce, tattaunawar cimma yarjejeniya tsakanin Washington da Kungiyar Kasashen Turai kan batun janye harajin ta gaza cimma nasara.

Mr. Ross ya kara da cewa, sabon tsarin biyan harajin zai fara aiki akan Canada da Mexico ne sakamakon dogon lokacin da ake ci gaba da dauka game da bitar yarjejeniyar kasuwanicin-bai-daya ta Arewacin Amurka, abin da ya ce, har yanzu babu wata tsayayyiyar ranar cimma matsaya a kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.