Ana ci gaba da aikin ceto a Guatemala

Yanzu haka dai ana ci gaba da aikin laluben mutanen da suka bace a cikin lakar wadda amon wutar ya haddasa.
Yanzu haka dai ana ci gaba da aikin laluben mutanen da suka bace a cikin lakar wadda amon wutar ya haddasa. AFP

Masu aikin agaji na can suna neman mutanen da suka bata a kasar Guatemala bayan da aka samu wani aman wutar da ya hallaka mutane akalla 25.Yanzu haka akwai tarin jama'a da ke ci gaba da karbar kulawar gaggawa bayan ceto su daga Ibtila'in wanda ya haddasa kwashe jama'a daga yankin da abin ke faruwa.

Talla

Rahotanni sun ce aman wutar ya haifar da laka mai zafi wadda ta kashe mutanen cikin su har da kananan yara da gidajen da ke Yankin.

David de Leon, mai magan da yawun hukumar agajin gagagwa ya ce an dakatar da aikin ceton daren jiya amma kuma an cigaba yau da safe ko za’a samu sauran mutanen da ke da sauran shan ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.