G7

Kasashen G7 sun yi wa manufofin Amurka tawaye

Kasashen G7 sun yi wa manufofin Amurka tawaye
Kasashen G7 sun yi wa manufofin Amurka tawaye REUTERS/BEN NELMS

Kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki wato G7 ta batsewa kasar Amurka sakamakon halin rashin tausayin da kasar ke nunawa wajen saka takunkumman karya tattalin arziki ga wasu hajojin da kasashen ke fitarwa a kasuwannin Duniya

Talla

Ministocin kudade daga kungiyar kasashen G7 masu karfin tattalin arziki a duniya, sun kammala taronsu a kasar Canada, inda gaba daya su ka yi kakkausar suka dangane da matakan da Amurka ke dauka a fagen kasuwanci, lamarin da ke kara jefa kasar rikici da sauran kasashen aminanta.

Taron na karshen mako dai ya kebe kasar Amurka saboda matakan karin haraji da take yi wa hajojin sauran kasashen gungun na G7.

Bill Morneau, shi ne ministan kudin kasar Canada mai masaukin baki a wannan taro, ya ce: 'Babbar manufar mu ita ce kokarin gamsar da Amurka domin ta jingine wannan sabon tsarin biyan haraji da ta daura wa kasashen abokannin huldarta.

Mun yi imani da cewa matakan da kasar ke dauka ba za su taba kawo ci gaba ga harkokin kasuwanci ko kuma na tattalin arziki a tsakanin mu ba.

Na tabbatar da cewa al’ummar Amurka kamar dai ‘yan uwansu na Canada, mafi yawansu ba sa goyon bayan wannan mataki na karin haraji'

A baya ma kasar Amurkar ta samu matsala tsakaninta da kasar China wadda ta kara wa harajin shigar da farin karfe a yankin Nahiyar Turai, a yayin da ita kuma a wani mataki namai da martani, ta lankaya wa duk wani abu da ake shigarwa kasar ta Chinadaga Amurka harajin sama da kashi 25, matakin da kuma bai yi wa Amurkar dadi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.