Isa ga babban shafi
Iran-Isra'ila

Netanyahu zai gabatarwa kasashen Turai 3 kudirinsa kan Iran

Gobe ake saran Netanyahu ya gana da shugaba Emmanuel Macron na Faransa, sai kuma Firaministan Birtaniya Theresa May ranar laraba.
Gobe ake saran Netanyahu ya gana da shugaba Emmanuel Macron na Faransa, sai kuma Firaministan Birtaniya Theresa May ranar laraba. REUTERS/Ronen Zvulun/Pool
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya fara ziyarar wasu kasashen Turai na kwanaki 3 daga yau litinin, inda ya isa Jamus domin tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar Iran wadda shugabannin kasashen ke kokarin cetowa.

Talla

Rahotanni sun ce Firaminista Benjamin Netanyahu zai yi kokarin shawo kan shugabannin kasashen Jamus da Faransa da kuma Birtaniya ne wajen komawa wani shiri na dabam kan yarjejeniyar Iran, sabanin wanda kasashen ke goyan baya.

Kafin barin Israila, Netanyahu ya ce zai gana da shugabanin kasashen 3 kuma zai gabatar musu ba batutuwa 2 da suka hada da Iran da kuma Iran, domin ganin an cigaba da matsawa kasar lamba.

Kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya na daga cikin kasashen da suka jagoranci kulla yarjejeniyar nukiliyar Iran a shekarar 2015, kuma har yanzu suna kan bakar su na goya bayan shirin duk da ficewar Amurka.

Gobe ake saran Netanyahu ya gana da shugaba Emmanuel Macron na Faransa, sai kuma Firaministan Birtaniya Theresa May ranar laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.