Guatemala

Ana ci gaba da neman mutane a Guatemala

Aman wutan dutsen Fuego a kasar Guatemala
Aman wutan dutsen Fuego a kasar Guatemala REUTERS/Luis Echeverria

Masu ayyukan ceto a kasar Guatemala na ci gaba da aikin nasu bayan aukuwar aman wuta daga dutse inda alkaluma na baya-bayan nan ke nuna mutane 75 aka karas da mutuwarsu

Talla

A kasar ta Guatemala,hukumar ayyukan ceto ta bayyana cewa mutane 200 ne yanzu haka an gaza sanin inda suka makale.

Aman wutan dutsen Fuego ya fara ne tun karshen makon daya gabata.

Gwamnatin kasar na ci gaba da aikewa da karin jami’an ta zuwa yankin domin kai dauki na musaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.