Isa ga babban shafi
Amurka

Yawan masu kashe kan su ya karu a Amurka

Wani da ya yi rashi
Wani da ya yi rashi REUTERS/Mohammad Ismail
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Hukumomin kula da lafiyar Amurka sun bayyana cewar an samu karuwar mutanen dake kashe kan su a kasar da kashi 30 daga shekarar 1999 zuwa yanzu, wanda alkaluma suka nuna cewar sun kai kusan mutane 45,000.

Talla

Wani rahoto da hukumar yaki da cututtukan kasar ta fitar ya bayyana kisan kai a matsayin babbar matsalar da ake fama da ita a bangaren kula da lafiya a cikin kasashe 44 daga cikin 50 dake fadin Amurka.

Ko a cikin wannan mako sanda fitacciyar mai yin jakankunan mata Kate Spade mai shekaru 55 ta kashe kan ta, matsalar da ta janyo hankalin jama’a da dama kan yadda mutane ke kashe kan su.

Mataimakin Daraktan kula da lafiya Anne Schuchat tace kisan kai ya zama bala’i ga iyalai da kuma al’ummomin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.