Isa ga babban shafi

ICC ta wanke Jean-Pierre Bemba daga aikata laifukan yaki

Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba
Tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba REUTERS/JERRY LAMPEN
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Kotun hukkunta masu manyan laifuka ta duniya ICC, ta soke hukuncin daurin shekaru 18 da yankewa tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Congo Jean-Pierre Bemba, bisa aikata laifukan yaki.

Talla

A shekarar 2016 kotun ta samu Bemba da laifin cin zarafin dan adam, baya ga sauran laifukan yaki, a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a shekarun 2002 da 2003, bisa zarginsa da gazawa wajen hana dakarunsa yi wa fararen hula kisan gilla da kuma aikata fyade.

Sai dai a lokacin da take sanar da soke hukuncin farkon, daya daga cikin alkalan kotun ta ICC, Christine Van den Wijingaert ta ce, alkalai a 2016, sun gaza la’akari da cewa Bemba ya yi iyaka kokarinsa wajen hana aikata laifukan yakin, bayan da aka sanar da shi abinda ke faruw, dan haka bai kamata a kamashi da laifin da wasu dakarunsa suka aikata ba.

Kungiyar kare hakkin dan adam da Amnesty International ta bayyana sabon hukuncin a matsayin gagarumin koma baya, ga akalla fararen hula 5,000 da suka rayu, bayan cin zarafin da mayakan Jean Pierre Bemba sukai musu.

A shekarar 2002, Bemba ya aike da sojoji 1, 000 cikin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, domin taimakawa shugaban kasar na waccan lokacin, Ange Felix murkushe wani yunkuri na yi masa juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.