Amurka

Amurka na cikin kasashen da ke cin zarafin mata a duniya

India ce kasa ta farko wajen fama da matsalar cin zarafin mata ta hanyar tirsasa musu lalata ko kuma yi musu fyade
India ce kasa ta farko wajen fama da matsalar cin zarafin mata ta hanyar tirsasa musu lalata ko kuma yi musu fyade SAJJAD HUSSAIN / AFP

Wani bincike ya bayyana Amurka a matsayin kasa daya tilo daga yammacin duniya daga cikin jerin kasashen duniya 10 da ke da hadarin rayuwa ga mata, bayan da aka kaddamar da wani shiri na ‘#Mee Too’ da ke bai wa mata damar fitowa fili don bayyana yadda aka ci zarafinsu.

Talla

Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya ce, binciken na wannan shekarar da masana harkokin mata 550 suka gudanar, ya bayyana Amurka a matsayin kasa ta 10 da aka fi samun matsalar cin zarafin mata, musamman ganin yadda mata a bangaren fina- finai ke ta fitowa fili suna bayyana yadda aka ci zarafinsu, ciki har da mai shirya fina-finai a Hollywood, Harvey Weinstein wanda yanzu haka, mata sama da 70 suka gabatar da kansu a matsayin wadanda suka fuskanci wannan matsala daga gare shi.

Jennifer Becker, wata lauya a Amurka ta ce,  yanzu haka mata sun samu baki ganin yadda daruruwa ke fitowa fili suna bayyana yadda suka fuskanci irin wannan matsala a wuraren ayyukan gwamnati da masana’antu.

Binciken wanda Gidauniyar Thomas Reuters ya gudanar ya nuna cewa, kasar India na kan gaba wajen cin zarafin mata ta hanyar tirsasa musu lalata ko kuma yi musu fyade, sai kuma Afghanistan da Syria da ke fama da yaki a matsayin kasashe na biyu da na uku wajen fama da matsalar, yayin da Somalia da Saudiya suka biyo baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.