Saudi-Yemen

Faransa na daukar nauyin taron agaza wa mutanen Yemen

Dan kasar Yemen dauke da buhun abincin agaji a birnin Sanaa
Dan kasar Yemen dauke da buhun abincin agaji a birnin Sanaa MOHAMMED HUWAIS / AFP

Yau laraba, ake fara taron kasa da kasa domin tattauna halin da al’ummar Yemen ke ciki sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun kawance karkashin jagorancin Saudiyya da kuma ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran.

Talla

Taron da zai gudana a birni Paris, gwamnatin Faransa ce ke daukar nauyin gudanar da shi, lura da halin matsi da milyoyin mutanen kasar ta Yemen suka tsunduma a wannan yaki da ya share tsawon shekaru ana gwabzawa.

To sai dai kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun nuna rashin amincewa da gayyatar wakilan gwamnatin Saudiyya zuwa wannan taro, saboda kasancewarta daya daga cikin masu hannu a rikicin.

A cikin gida Faransa ma akwai masu adawa da taron kamar Sebastien Nadot, dan majalisar dokoki daga jam’iyya mai mulki La Republique en Marche, ya ce wannan taro ba wai an shirya shi ne domin kula da matsalolin al’ummar kasar Yemen ba, domin kuwa an gayyaci ‘yan siyasa da masu bayar da agaji ne a maimakon wadanda ke fama da matsala sakamakon wannan yaki zuwa taron na birnin Paris ba.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.