Amurka

Shirin hana baki daga kasashen musulmi biyar shiga Amurka ya tabbata

Donald Trump, shugaban Amurka
Donald Trump, shugaban Amurka 路透社。

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana samun gagarumar nasara a shirinsa na hana baki daga kasashe biyar na musulmai zuwa kasar sakamakon wani hukuncin kotun koli da ya amince da matakin.

Talla

Alkalai 5 suka kada kuri’ar goyan bayan shirin, yayin da 4 suka ki amincewa da shi, abin da ke tabbatar da nasarar Trump a wannan takun-saka da na tsawon watanni tsakanin shugaban da wadanda ke kallon matakin a matsayin wanda ya yi hannun riga da matsayin Amurka na kasa jagora a tattalin arziki da kuma siyasar duniya.

Wannan mataki zai shafi baki ‘yan kasashen Iran, Libya, Somalia, Syria da kuma Yemen, sai Koriya ta Arewa wadda shugaban ya sanya ta a cikin shirin.

Trump ya ce ya dauki mataki ne domin tabbatar da tsaron Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.