Amurka-Jarida

'Yan jarida 5 sun mutu a harin da dan bindiga ya kai musu a Amurka

Jarrod Ramos, wanda ake zargi da kisan ma'aikatan Jaridar Gazette 5 bayan kai hari ofishinsu da ke Annapolis da ke Maryland a Amurka.
Jarrod Ramos, wanda ake zargi da kisan ma'aikatan Jaridar Gazette 5 bayan kai hari ofishinsu da ke Annapolis da ke Maryland a Amurka. Reuters/路透社

Hukumomin Amurka sun tabbatar da mutuwar mutane biyar lokacin da wani dan bindiga ya kutsa kai dakin hada labaran wata Jaridar Annapolis dauke da gurneti inda ya bude wuta kan mai uwa da wabi.An bayyana cewa maharin farar fata ne mazaunin Maryland.

Talla

Wami ma’aikacin jaridar Capital Gazette wadda take aiki tun karni na 18, ya aike da sako ta twitter yana bayanin yadda Dan bindigar ya yi harbi ya kuma fasa gilashin kofar ofishin Jaridar kafin bude wuta kan ma’aikatan ta.

Phil Davis, mai dauko labaran ayyukan da suka shafi laifuffuka ya ce babu abin takaicin da ya wuce jin karar yadda ake harbe mutane, yayin da kake labe a karkashin teburin ka, kafin daga bisani ka ji dan bindigar na dada loda harsasai domin cigaba da harbin jama’a.

Shugaban Yan Sanda, Anne Arundel ya tabbatar da kasha mutane 5, yayin da wasu biyu suka jikkata.

Jaridar Baltimore Sun da ta mallaki Capital Gazette ta bayyana dan bindigar a matsayin Jarrod Ramos, wanda ya dade yana takun saka da Jaridar kan wani labari da ta wallafa a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI