MDD-MYANMAR

Gutteress ya koka da halin da 'Yan gudun hijirar Rohingya ke ciki

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a ziyarar da ya kai sansanin Kutupalong da ke Cox's Bazar a Bangladesh wurin da 'yan gudun hijirar na Mynamar ke samun mafaka.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a ziyarar da ya kai sansanin Kutupalong da ke Cox's Bazar a Bangladesh wurin da 'yan gudun hijirar na Mynamar ke samun mafaka. REUTERS/Mohammad Ponir Hossain

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterress, ya ce halin da 'yan gudun hijirar musulmi ‘yan kabilar Rohingya ke ciki abin takaici haka zalika ya zama wajibi a tuhumi gwamnatin Myanmar kan kisan kare dangi da kuma azabtarwar da jami'an tsaron kasar suka yiwa musulman 'yan Rohingya. 

Talla

Guterres wanda ke wannan batu bayan ganawarsa da 'yan gudun hijirar ta Rohingya wadanda ke samun mafaka a Bangladesh yau litinin ya ce 'yan gudun hijirar ta Rohingya na tsananain bukatar agaji fadi hakan ne, a ziyaran da yakai sansanin ‘yan gudun hijirar Bangladesh a yau Litinin.

Antonio Guteresh ya kwatanta yanayin take hakkin bil’adama a matsayin mafarki ga waɗanda jami’an tsaron Miyammar suka tilasta tserewa daga gidajensu a bara, a binda Majalisar Dinkin Duniyar ta kira yunkuri kawar da wata kabila daga doran kasa.

‘Yan gudun hijirar da ke sansanin mafi girma a duniya na Kutupalong a Bangladash, wanda ke dauke da ‘yan gudun hijira fiye da miliyan daya, sun shaidawa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar irin wulakancin da suka fuskanta na Fyade da cin zarafi iri-iri na tashin hankali.

Guteresh ya ce, abin da aka yi wa musulmai ‘yan kabilar Rohingya na daga cikin take hakkin bil-adama mafi muni a tarihin wannan karnin.

Fiye da ‘yan kabilar Rohingya 700,000 ne suka nemi mafaka a kasar Bangladash a watan Agustan da ya gabata, sakamakon kisan kare dangin da jami’an tsaron Myanmar ke musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.