Isa ga babban shafi

Kagame ya fitar da 'yar takararsa ga kungiyar Francophonie

Ana saran gudanar da taron Francophonie a ranar 11 ga watan Oktobar shekarar nan domin zaben sabbin shugabannin ta Armenia.
Ana saran gudanar da taron Francophonie a ranar 11 ga watan Oktobar shekarar nan domin zaben sabbin shugabannin ta Armenia. Francois Mori/Pool via Reuters
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Azima Bashir Aminu
Minti 2

Shugabannin Kungiyar kasashen Afirka sun bayyana goyan bayan su ga takarar Ministan harkokin wajen Rwanda Loisue Mushikiwabo a matsayin Sakatare Janar na kungiyar kasashen masu amfani da harshen Faransanci na Francophonie.

Talla

Rahotanni daga wajen taron shugabannin kungiyar kasashen Afirka da ya kammala a Nouakchott da ke Mauritania sun ce shugabannin kasashen sun amince da takarar Loiuse Mushikiwabo a matsayin yar takarar kujerar Sakatariyar kungiyar kasashe renon Faransa da za’ayi nan gaba.

Wannan mataki ya biyo bayan gayyatar wakilan kungiyar zuwa taron domin gabatar musu da takarar jami’ar diflomasiyar Rwandar domin maye gurbin Michelle Jean, yar kasar Canada wadda ke kammala wa’adin ta na farko na shekaru 4 a watan Oktoba mai zuwa.

Kafin fara taron shugabannin Afirka, shugaban Rwanda Paul Kagame da ke jagorancin kungiyar AU ya gabatar da takarar ministar harkokin wajen sa wanda ya samu goyan bayan shugaba Emmanuel Macron na Faransa wanda ya bayyana aniyar sa na ganin kujerar ya je Afirka.

Ana saran gudanar da taron Francophonie a ranar 11 ga watan Oktobar shekarar nan domin zaben sabbin shugabannin ta Armenia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.