Bakonmu a Yau

Garba Shehu kan ziyarar Macron a Najeriya

Sauti 03:33
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari Présidence du Nigéria /Reuters

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi alkawarin bayar da tallafin Dalar Amurka miliyan 75 don ci gaba da yaki da kungiyar Boko Haram a Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita. Macron wanda a karon farko kenan da yake ziyartar Najeriya a matsayin shugaban kasa, ya ce, gwamnatinsa za ta kuma bai wa Najeriyan bashin kudaden da yawansu ya kai Dala miliyan 475 don inganta harkokin sufuri a jihar Legas da samar da ruwan sha mai tsafta a jihar Kano, yayin da kuma za a bunkasa gandun dajin da ke jihar Ogun. Kabir Yusuf ya tattauna da mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu wanda ya yi fashin baki kan ziyarar.