Thailand

An kubutar da dukkanin yaran da suka makale a kogon Thailand

A ranar 23 ga watan jiya ne, yaran da shekarunsu ke tsakanin 11 zuwa 16 da kuma kocinsu mai shekaru 25, suka shiga cikin kogon Tham Luang a dai dai lokacin da ake tafka ruwa kamar da bakin-kwarya bayan sun kammala atisayen kwallon kafa.
A ranar 23 ga watan jiya ne, yaran da shekarunsu ke tsakanin 11 zuwa 16 da kuma kocinsu mai shekaru 25, suka shiga cikin kogon Tham Luang a dai dai lokacin da ake tafka ruwa kamar da bakin-kwarya bayan sun kammala atisayen kwallon kafa. Twitter @elonmusk/via REUTERS

Hukumomi a Thailand sun tabbatar da ceto sauran yara 5 da suka rage a kogon kasar yau din nan bayan tun farko an iya ceto 13 da Kociyansu. Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka ilahirin yaran na karbar kulawar gaggawa a Asibiti la'akari da yadda suke a galabaice.

Talla

Cikin wasu bayanai da ta wallafa a shafinta na Twitter rundunar sojin ruwan kasar ta ce an kubutar da ilahirin yaran ko da dai wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali haka zalika jami'i guda ya rasa ransa.

A ranar 23 ga watan jiya ne, yaran da shekarunsu ke tsakanin 11 zuwa 16 da kuma kocinsu mai shekaru 25, suka shiga cikin kogon Tham Luang a dai dai lokacin da ake tafka ruwa kamar da bakin-kwarya bayan sun kammala atisayen kwallon kafa.

A ranar 24 ga watan na jiya ne, jami’an tsaro suka gano sahun kafa da na hannu na wadannan yara a hanyar kogon, lamarin da ya sa aka fara gudanar da aikin neman su.

A ranar 25 ga watan Yuni ne, wasu sojin ruwa kuma gwanayen ninkaya suka kutsa cikin kogon, yayin da aka kafa wata rumfar wucen-gadi don gudanar da addu'o'in ceto yaran.

A ranar 26 ne kuma, gwanayen ninkayar suka isa wata mahadar hanya mai tazarar kilomita mai yawa zuwa cikin tsakiyar kogon, amma sun gaza karasawa ciki saboda ambaliyar ruwa wadda ta toshe mashigin wurin da yaran suka fake.

A kashe-garin ranar ne, wata tawaga da ta kunshi kwararru daga Amurka da Birtaniya ta iso Thailand don ceto yaran.

Bayan shafe wasu ‘yan kwanaki , gwanayen ninkaya suka yi nasarar gano yaran 12 da kocin nasu a raye, yayin da a ranar 3 ga wannan wata aka isar da abinci da magunguna ga yaran duk da cewa, za su ci gaba da zama a cikin kogon kafin kammala dabarun futo da su.

Sai dai a ranar Lahadi ne aka fara ceto yaran daya bayan daya inda aka kammala aikin ceton a yau Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.