Eritrea

Za a cire wa Eritrea takunkumi saboda Habasha

Firaministan Habasha Abiy Ahmed da shugaban Eritrea Issayas Afewerki sun cimma matsayar dinke barakar da ke tsakanin kasashen biyu
Firaministan Habasha Abiy Ahmed da shugaban Eritrea Issayas Afewerki sun cimma matsayar dinke barakar da ke tsakanin kasashen biyu ASHRAF SHAZLY, Sumy SADRUNI / AFP

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana bukatarsa ta ganin an cire wa kasar Eritrea takunkumin da aka kakaba ma ta sakamakon yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kulla da makociyarta Habasha.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai a ziyarar da yake yi a yankin, Guterres ya ce, takunkuman da aka dora wa Eritrea sun biyo bayan wasu batutuwa da dama da suka faru, amma shi a ganinsa yanzu haka wadancan batutuwa sun kau, saboda haka ya dace a janye su.

Sakataren na ziyara a Habasha ne kwana guda bayan Firaminista Abiy Ahmed ya ziyarci shugaba Isaias Afwerki na Eritrea, in da suka kulla sabuwar dangantakar diflomasiya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

A bangare guda, ana saran jirgin saman fasinja na farko ya isa Eritrea daga Habasha a ranar Talata, wanda a karon farko kenan da hakan ke faruwa cikin shekaru 20 da kasashen biyu suka kwashe suna rikici da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.