Turai

Belgium ta doke Ingila a wasan neman matsayi na uku

Karawar Belgium da Ingila a gasar cin kofin Duniya na Rasha
Karawar Belgium da Ingila a gasar cin kofin Duniya na Rasha REUTERS/Fabrizio Bensch/File Photo

Kasar Belguim ta lashe tagullar gasar cin kofin duniyar dake gudana yanzu haka a Rasha, bayan ta doke Ingila da ci 2-0 a wasan neman matsayi na uku.

Talla

Meunier ya fara jefawa Belgium kwallon ta na farko mituna 4 da fara wasa, yayin da Eden Hazard ya jefa ta biyu a mituna 82.

Shugaban hukumar kwallon kafar Duniya Gianni Infantino ya yaba da irin kokarin da kungiyoyin kasashen biyu suka yi a wannan karawa.

Wannan nasara ta baiwa Belgium matsayi na uku a gasar, yayin da gobe ake karawar karshe tsakanin Faransa da Croatia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.