Amurka-Rasha

Trump na ganawar keke da keke da Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka, Donald Trump
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka, Donald Trump Sputnik/Mikhail Klimentyev/Kremlin via REUTERS

Shugaban Amurka Donald Trump zai yi ganawar keke da keke da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a ranar Litinin a birnin Helsinki bayan shafe tsawon watanni ana dakon wannan ganawa tsakanin shugabannin biyu masu banbancin ra’ayi kan wasu batutuwa.

Talla

Ana kallon wannan ganawa a matsayin zakaran gwajin-dafi ga burin shugaba Donald Trump na kulla dangantaka tsakaninsa da shugaba Vladimir Putin na Rasha.

Muddin wannan ganawa ta haifar da da mai ido, to babu shakka hakan zai iya sassauta wasu tashe-tashen hankula da ake fargabar aukuwarsu a duniya.

Sai dai kasashen Amurka da Rashan na da dadadden tsamin dangantaka, kuma akwai wasu batutuwa da dama da ka iya haifar da cikas ga yunkurin shugaba Trump na samar da kyakkyawar alaka tsakaninsa da Putin.

Kasashen biyu sun samu sabani kan wasu batutuwan da suka shafi Syria da Ukraine da batun leken asirin kasa har ma da kutsen Rasha a zaben Amurka, yayin da shugaba Trump ya ce, zai halarci ganawar ne amma ba da wasu manyan burika da yake fatan cimma ba.

Sai dai duk da haka, Trump ya ce, yana ganin ya dace a yi wannan ganawa wadda za ta gudana ba tare da wata takamammiyar ajanda da shugabannin biyu za su tattauna akai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.