EU da Trump sun fara sasantawa kan yakin kasuwanci

Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban hukumar kungiyar Tarayyar Turai yayin tattaunawarsu da ta kai ga janye wasu rigingimun kasuwanci da ke tsakanin Amurka da kungiyar.
Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban hukumar kungiyar Tarayyar Turai yayin tattaunawarsu da ta kai ga janye wasu rigingimun kasuwanci da ke tsakanin Amurka da kungiyar. REUTERS/Kevin Lamarque

Amurka da kungiyar kasasshen Turai EU, sun cimma matsayar kaucewa cikakke fito na fito na yakin kasuwanci, ta hanyar rage haraji da suka kakabawa kayayyakin da suke kaiwa kasuwannin junansu.

Talla

Cimma matsaya, ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban hukumar kungiyar tarayyar turai, Jean-Claude Juncker, wanda ya gudana jiya Laraba a fadar White House.

Bayan tattaunawar ce shugaban Trump ya sanar da janye aniyarsa ta kakaba sabon haraji kan motocin da kasashe turai ke shigarwa Amurka.

Sai dai harajin kashi 25% da kuma na kashi 10% da gwamnatin Trump ta kakaba kan karafa da aluminium da kasashen turan ke kaiwa kauwannin Amurka tun a watan Maris na wannan shekara, zai ci gaba da aiki.

A baya bayan nan dai, shugaba Trump na fuskantar matsin lamba daga Amurkawa, biyo bayan martanin da kasashen Mexico, China, Canada da kuma kungiyar tarayyar turai EU, suka maidawa manufofin Trump kan kasuwanci, ta hanyar kakaba jerin haraji kan kayayyakin da Amurka ke shigarwa kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.