An yi kusufin wata mafi tsawo a tarihin duniya

Hoton yadda kusufin wata ya bayyana a birnin Ashkelon, na kasar Isra'ila. 27 ga watan Yuli, 2018.
Hoton yadda kusufin wata ya bayyana a birnin Ashkelon, na kasar Isra'ila. 27 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Amir Cohen

An samu aukuwar kusufin wata mafi tsawo da aka taba gani a tarihin duniya cikin karni na 21.

Talla

Kusufin na wata mafi tsawo da ya auku a ranar Juma’a, 27 ga watan Yuli, 2018, ya shafe Sa’a 1, da mintuna 42, da kuma dakika 57.

Sassan da kusufin ya fi bayyana sun hada da nahiyar Turai, Afrika, Yankin Gabas ta Tsakiya, nahiyar Asiya, sai kuma Australia da Rasha, kamar yadda hukumar binciken sararin samaniya ta NASA ta tabbatar.

Masana ilimin taurari sun yi hasashen cewa za’a sake samun aukuwar makamancin kusufin na wata ne wani lokaci cikin shekara ta 2123.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.