Isa ga babban shafi
Amurka

Kamfanin Apple ya zama na farko da ya mallaki jarin dala tiriliyan guda

Des militants d'Attac manifestent contre Apple devant le Palais de justice de Paris, le 12 février 2018.
Des militants d'Attac manifestent contre Apple devant le Palais de justice de Paris, le 12 février 2018. REUTERS/Charles Platiau
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu | Abdoulkarim Ibrahim
Minti 2

Kamfanin Apple ya kasance na farko da ya mallaki jarin da yawansa ya kai dala Triliyan daya a tarihin kasuwar hannayen jarin kasar Amurka.

Talla

A yau alhamis ne kamfanin ya kai ga wannan matsayi, bayan da aka sayar da hannun jarinsa daya akan dalar Amurka 207 a kasuwar hannayen jari mafi girma a duniya da ke birnin New York wato Wall Street.

Wani lokaci a 2007 hannun jarin kamfanin PetroChina ya taba samun irin wannan daraja ta gajeren lokaci, amma duk da haka bai mallaki dukiyar da yawanta ya kai dala triliyan daya ba.

Wannan daraja da kamfanin na Apple ya sama za ta kara daukaka kima da darajar kasuwar hannayen jarin New York a cewar Howard Silverblatt wanda masani ne a daya daga ciin kasuwannin birnin wato Dow Jones,

Masana dai na ganin cewa ko ba komai, wannan daraja za ta kara janyo hankulan masu saka jari a kamfanin na Apple wanda ya shahra ta fannin ayyukan sadarwa, kera wayoyi da kuma samar da man haja.

Wani lokaci a baya, shugaban kamfanin Microsoft kuma attajirin duniya Bill Gates, ya bayyan Apple a matsayin wanda ke jan hankula masu saka jari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.