Saudiya-Canada

Saudiya ta kori jakadan Canada

Mai rajin kare hakkin bil'adama Samar Badawi tare da Michelle Obama da Hillary Clinton
Mai rajin kare hakkin bil'adama Samar Badawi tare da Michelle Obama da Hillary Clinton Wikipedia

Kasar Saudi Arabia ta bai wa Jakadan Canada sa’oi 24 da ya fice daga kasar, yayin da ta umurci nata Jakadan da ya koma gida bayan katse harkokin kasuwanci da zuba jari tsakanin kasashen biyu.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Canada ta bukaci sakin masu rajin kare hakkin bil'adama da take zargin Saudiya da tsarewa, cikinsu har da fitacciyar mai fafutukar kare hakkin bil'adama 'yar asalin Saudiya da Amurka, wato Samar Badawi.

Mahukuntan Saudiya na kallon kiran da Canada ta yi a matsayin katsalandan kan harkokinta na cikin gida.

Wannan ya dada fito da irin matakan diflomasiyar da Yarima Mohammed bin Salman ke dauka.

A makon jiya ne Canada ta bukaci sakin mata da masu kare hakkin bil' adama cikin gaggawa da take zargin Saudiyar da tsarewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.