Isa ga babban shafi
Masar-Saudiya

Masar ta goyi bayan Saudiya kan rikicinta da Canada

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-sisi yayin ganawarsa da Sarki Salman na Saudiyya.
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-sisi yayin ganawarsa da Sarki Salman na Saudiyya. Reuters
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Kasar Masar ta bayyana goyon bayanta ga Saudi Arabia dangane da rikicin diflomasiyar da ya barke sakaninta da Canada saboda abinda Saudiyar ta kira katsalandan kan harkokin ta na cikin gida.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana damuwa kan rikicin da ke tsakanin kasashen biyu, wadda ta danganta shi kan yadda kasashen duniya ke katsalandan kan harkokin cikin gida na wasu kasashen.

Ita kan ta Masar ta fuskanci irin wannan matsala, na zargin take hakkin Bil Adama, wanda ya sa Amurka ta dakatar da agajin da ta ke bata, kafin sauya matsayi a watan jiya.

Bayan barkewar rikicin Diflomasiyyar tsakanin Saudiyya da Canada Amurka ta nuna bukatar shiga tsakani sai dai ana ganin batun ya fara munin da ba zai sasantu cikin sauki ba.

Ko a daren jiya Talata gwamnatin Saudiyyar ta bai wa jakadan Canada da ke birnin Riyadh wa'adin yau laraba ya tattara kayansa don ficewa daga kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.