Venezuela-Ecuador

Al'ummar Venezuela rabin milyan sun yi hijira zuwa Ecuador a bana

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijirar daga farkon shekarar nan zuwa yanzu akalla al’ummar Venezuela dubu dari biyar da 47 ne suka tsallaka Ecuado.
A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijirar daga farkon shekarar nan zuwa yanzu akalla al’ummar Venezuela dubu dari biyar da 47 ne suka tsallaka Ecuado. SCHNEYDER MENDOZA / AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da al’ummar Venezuela dubu dari biyar ne suka suka tsallaka iyakar kasar da Ecuador bayan da Kasar ta sanya wata dokar ta baci don tallafa ‘yan gudun hijirar Venezuelan da talauci ke rabowa da kasarsu.

Talla

Kasashen Colombia da Brazil wadanda suka hada iyaka da Venezuelan mai fuskantar mafi munin matsalar tattalin arziki sun kaddamar da wani shirin agajin gaggawa don kare Venezuelan daga durkushewa baki daya.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majlisar dinkin duniya yayin taron da ta gudanar a birnin Geneva, ta ce a dai dai lokacin da tsananin talaucin ke kara ta’azzara sakamkon tabarbarewar tattalin arzikin a Venezuela adadin ‘yan gudun hijirar da ke shiga Ecuado ya karu yayin da wasu ke tafiya da kafafuwansu inda suke shafe akalla makwanni biyu kafin tsallakawa Quito.

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijirar daga farkon shekarar nan zuwa yanzu akalla al’ummar Venezuela dubu dari biyar da 47 ne suka tsallaka Ecuado.

A cewar hukumar, matakin na gwamnatin Ecuado wajer bayar da matsugunai da kuma samar da wani asusun tallafawa ‘yan gudun hijirar Venezuelan ya taimaka matuka, wanda kuma Majalisar Dinkin Duniya ma na gab da yin makamancin yunkurin.

Sai dai duk da wannan mataki na kasashen shugaba Nicolas Maduro na Venezuela na ci gaba da kallon shugabannin kasashen makwabtan na shi a matsayin makiya, ko da dai kawo yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalar karancin abinci da magunguna a kasar mai fama da matsalar tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.