Myanmar

"Ya kamata shugabar Myanmar ta yi murabus"

Ana zargin shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi da kin daukan mataki kan kisan kiyashin da sojoji suka yi a Rohingya
Ana zargin shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi da kin daukan mataki kan kisan kiyashin da sojoji suka yi a Rohingya REUTERS/Soe Zeya Tun

Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya mai bari gado, Zeid Ra’ad al-Hussain ya ce, tuntuni ya kamata shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta yi murabus saboda yadda sojojin kasar suka yi wa Musulmin Rohingya kisan kiyashi.

Talla

A cewar Hussain, abin takaici ne yadda shugabar ke kokarin kafa hanzari game da ala’amarin saboda a cewarsa tana da ikon daukan mataki.

Kalaman Ra’ad na zuwa ne bayan rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da ke cewa, sojojin Myanmar sun yi wa ‘yan kabilar Rohingya kisan kiyashi tare da aikata fyade kan matansu.

Sai dai tuni Myanmar ta yi watsi da rahoton wanda ta bayyana a matsayin mai cike da kare-rayi.

Rahoton ya zargi Suu Kyi da gazawa wajen magance tashin hankalin wanda ya tilasta wa dubban al’ummar Rohingya ficewa daga kasar.

A bangare guda, hukumar da ke bada lambar girma ta Nobel ta duniya ta ce ba ta tunanin karbe lambar da aka bai wa Suu Kyi duk da wannan rahoto na Majalisar Dinkin Duniya.

Daraktan hukumar, Olav Njolstad ya ce, dokar hukumar ba ta amince da janye lambar kyautar ba.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres tare da Jakadun kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da Sweden duk sun bukaci hukunta shugabannin sojin Myanmar kan rawar da suka taka wajen kisan kiyashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.